Babu Albashi Ga Duk Wanda Ya Shiga Yajin Aiki - Labarai Ingantattu

AdSense

Babu Albashi Ga Duk Wanda Ya Shiga Yajin Aiki

Majalisar Zartaswar Nijeriya ta zartas da dokar babu aiki, ba albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya. Ministan kwadago da daukar aiki, Dakta Chris Ngige ne ya bayyana haka jiya jim kadan bayan kammala zaman Majalisar zartaswar tarayya a fadar Shugaban Kasa dake Abuja. Ya ce, wannan doka ta biyo bayan takardar rahoton da kwamitin binciken yajin aikin ma’aikatan gwamnatin tarayya ya gabatar.
Ngige ya ce; sashen ma’aikatan gwamnati ya jima yana fuskantar matsaloli; wanda ta kai gwamnatoci suka yi ta kafa kwamitoci domin a shawo kan matsalar yajin aiki da ake yawan samu.
Ministan ya bayyana cewa kwamitin kwararrun, wanda aka rantsar da shi a ranar 27 ga watan Afrilun 2016 ya yi aikinsa, ya kuma gabatar da rahoto a gaban majalisar zartaswar tarayya a watan Oktobar shekarar 2017.
“Majalisar zartaswar tarayya bayan ta amshi wannan rahoton, ta fitar da kwamitin mutum goma wanda nake shugabanta, mu ne muka rubutawa gwamnati farar takarda akan abubuwan da kwamitin kwararrun ya kawo.” inji shi Ministan ya kara da cewa, abin da doka ta ce, shi ne duk wanda bai yi aiki ba, ba za a biya shi na tsawon lokacin da bai wannan aikin ba. Haka kuma a wannan tsawon lokacin da ma’aikaci ya diba ba ya wurin aiki za a cire adadin kwanakin a yayin da aka zo biyansa kudin fensho a matsayinshi na ma’aikacin gwamnati.
Ya ce, Majalisar zartaswar tarayya ta amshi wannan takarda daga hannunsu a matsayin wacce ke dauke da tataccen bayani, saboda hatta kotun ma’aikata ma ta zayyana irin wannan doka a dokokinta.

No comments

Powered by Blogger.