EFCC Ta Saki Hotunan Kadarorin Tsohon Gwamna Fayose - Labarai Ingantattu

AdSense

EFCC Ta Saki Hotunan Kadarorin Tsohon Gwamna Fayose

EFCC ta saki hotunan kadarorin tsohon gwamna Fayose
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya amsa gayyatar hukumar EFCC a ranar Talata sakamakon karewar kariyar da yake da ita a matsayinsa na gwamna bayan wa’adin mulkinsa ya kare, inda ya sha tambayoyi da binciken kwakwkwafi.
Jaridar ThePunch ta rawaito cewar a yayin da aka shigar da Fayose dakin binciken na EFCC, jami’an hukumar sun bukaci ya rubuta duk abinda ya sani da kuma yadda ya kashe makudan kudade da suka kai naira biliyan N1.3b da suka ce ya karba daga ofishin Sambo Dasuki gabanin zaben jihar na 2014.
Majiyarmu ta rawaito wani jami’in hukumar na bayyana mata cewa hukumar EFCC ta bukaci tsohon gwamna Fayose ya dawo da wadannan kudade domin haramtattu ne da aka fitar da su ba bisa ka’ida ba.
Sai dai Fayose yayi tirjiya, inda yace bai amshi ko sisi daga Sambo Dasuki ba.
Ana cikin wannan dambarwa ne sai hukumar ta EFCC, a jiya,Laraba, ta saki hotunan wasu manyan kadarori da Fayose ya mallaka a manyan unguwannin birnin Abuja da Legas.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya aike da hotunan ga kafafen yada labarai tare da sanar da su cewar hukumar ce ta binciko kadarorin da Fayose ya mallaka lokacin da yakegwamna a jihar Ekiti.
Yanzu haka tsohon gwamna Fayose ya kwana biyu a ofishin hukumar EFCC, adadin kwanakin da ya bar gidan gwamnatin jihar Ekiti.
Tun a ranar Talata da ya amsa gayyatar EFCC, Fayose ya isa ofishin hukumar rataye da jakarsa, wacce ya ce ta na dauke da mayafansa na kwanciya da komatsan sa na amfani.

No comments

Powered by Blogger.