GANDUJE Shine Gwamna Mafi Aiki A Nageriya Inji Kungiyar ISMOG - Labarai Ingantattu

AdSense

GANDUJE Shine Gwamna Mafi Aiki A Nageriya Inji Kungiyar ISMOG

GANDUJE shine Gwamna mafi aiki a nageriya inji kungiyar ISMOG
Daga M Inuwa MH
Yaudai Bari Mu Fadi Kadan Daga Cikin Aikin Da Ganduje Yayima Kano
Shahararriyar kungiyar nan ta international social media organization groups ISMOG
Wato kungiyar datayi fice wajen
Binciken abinda shuwa gabanninku suke shuka maku afadin tarayyar nageriya nan
Walau na alkhairi
Ko Akasin haka kungiyar karkashin jagorancin shugaban ta wato M INUWA MH
Ta bayyana gwamnan kano Dr abdullahi umar Ganduje amatsayin gwamnan dayafi ko wanne
Gwamna aiki a acikin gwamnonin da aka zaba a 2015 nageriya.
Kungiyar ta kira gwamna Ganduje amatsayin gorzon shekarar 2016 data gabata
Tayi kuma kira ga sauran gwamnoni da suyi koyi da gwamna Ganduje wajen aikatawa
Jihohinsu aiyukan alkhairi
Irin na gwamna gandujen.
Kungiyar ta ISMOG tace bata jinjinama gwamna Dr abdullahi Umar ganduje haka kawai ba a.a
Saida tayi binciken wainar dayake toyawa ajihar tasa daga bisani ta bashi lambar yabo.
Kungiyar ISMOG ta bayarda misali kamar haka…
*Ya Karasa Babban Aikin Gadar Kasa Ta Kofar Kabuga Wacce Taci Makudan Kudade…
*Ya Bada Umarnin Cigaba Da Aikin Gadar Sama Dake Murtala Muhammad Way Sabon Gari Wacce Ita ma Take Lashe Makudan Kudade…
*Ya Bada Damar Karasa Asibitin Yara Dake Zoo Road Da Yankaba Dukkan Asibitocin Suna Lashe Manyan Kudade
*Ya Bada Umarnin Cigaba Da Aikin Gadar Kasa Dake Kofar Gadan Kaya Wacce Itama Take Lashe Manyan Kudade..
*Duk Da Irin Halin Matsin Tattalin Arziki Da Ake Ciki A Nigeria. ..
*Gwamna Ganduje Ya Kirkiri Sabon Aikin Gadar Kasa A Mahadar Titin Sheikh Jaafar Mahmoud Dake Kwanar Fanshekara Wacce Tuni Aikin Yayi Nisa Sosai….
*A Yanzu Haka Ankusa Gama Sabon Titi Mai Hannu Biyu A Unguwar Gorandutse Zuwa Jakara
*Sannan Angama Sabon Titi Mai Hannu Biyu Tare Da Fitila A Unguwar Kwanar Taya Dake Kofar Dawanau. …
*Gwamna Ganduje Tuni Ya Tura Matasa Guda 73 Garin Kaduna Don Su Koyo Yadda Ake Gyaran Mota A Zamanance Wato Gyara Da Computer
*Sannan Ya Tura Wadansu Matasan Kasar Turkey Sun Koyo Yadda Ake Kiwon Shanun Zamani…
*Rabawa kungiyoyi kayan aikin gayya kyauta
Kaddamar da rabawa jama’a magani kyauta a ma’ajiyar gwamnti dake karamar hakumar Ungoggo.
*Bayar da kwangilar hanyar Dantsawa zuwa Zainawa akan kudi naira milyan 319.
*Sayo gadaje da katifu tare da rabawa asibitan jihar ta Kano.
*Karasa gadar sama mai suna Gadar Lado dake Zaria Road
*Samar da ruwa kauyan Dan zabuwa
*Kudurin ajiye tankin ruwa na duidindin a kowacce kasuwa tare da motatocin kashe gobara domin magance gobara
*Aikin titi karamar hukumar Minjibir mai nisan kilo mita 5
*Karasa aikin binne bututun ruwa dake Tanburawa
*Aikin asibitin yara domin ingantuwar lafiya a jihar
*Aikin titin Kofar Ruwa/Tudun Fulani, Bachirawa zuwa Kadawa Miltara
*Daukar mutin 140 domin basu tallafi a kowacce karamar hakuma dake jihar ta Kano
*Titin kasa na barikin sojojin dake Vakabo
*Aikin titin Daura zuwa Danbatta
*Bunkasa wajen casar alkama
*Gina hanyar Dakata zuwa Bella
*Aikin gina gidaje mai suna Kundila Estete dake karamar hukumar Tarauni
*Aikin gadar da ta hade kananan hukumomi bakwai wato Kumbotso, Tofa, Rimin Gado, Kabo ta bulle Karaye da wani sashi na Rogo
*Aikin Kofar Dawanau da ya bulle Dawakin Tofa
*Aikin ido da bayar da magani da gilasai sama da mutun dubu biyar
*Aikin gadar kasa da babu salon irin ta a fadin kasar nan dake Fanshekara
*Akin sabunta titin Magwan
*Gina masallacin Juma’a dake Zaitawa dake karamar hakumar Gezawa
*Gina hanya da za ta sadu da kananan hukumomi 10mai nisan kilo mita70.
*Gina hanaya Maiduguri jikin Moble Barack
*Ware naira milyan 48.4 domin magance lassa da maleria a fadin jihar.
*Gyara titin Farm Centre
*Da magance zaizayar kasa a makaratar Gayawa dake karamar hukumar Nasarawa
*Titin Boss Katsina Road…
*Gyaran hanyar Burum-burum Kibiya Rano Karfi road
*Gina hanyar Tiga Rurum Rano
*Samar da motocin shara masu suna Kano Kal-kal..
*Aikin titin CBN Kwatas
*Gadar sama dake ‘Yan Kura zuwa Bakin Wafa..
*Samar da shinkafa tare da niyyar samar da kaso 50%cikin dari na shinkafar da za’ayi anfani da ita a nageriya
Zamuyi Sati Guda Muna Fadan Aikin Ganduje Ga Kanawa
Da fatan gwamnoninmu zasuji kira

No comments

Powered by Blogger.