Har Yanzu Babu Kamar Faransa A Duniya, Cewar Griezman - Labarai Ingantattu

AdSense

Har Yanzu Babu Kamar Faransa A Duniya, Cewar Griezman

Antoine Griezmann ya ceto kasar Faransa daga shan kaye a wasan da suka fafata daren ranar Talata tsakaninsu da kasar Jamus, inda Faransa ta samu nasara da kwallaye 2-1, a sabuwar gasar kasashe ta Nations League da hukumar UEFA ta fara shiryawa.
Dan wasan Jamus, Toni Kroos ne ya soma jefa kwallo a ragar Faransa, bayan samun damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma daga bisani Grizemann ya zura kwallaye biyu a ragar Jamus.
Griezmann ya ci kwallon farko ne da kai, yayinda ya jefa ta biyu, bayan samun damar bugun daga kai sai tsaron gida kamar yadda itama Jamus din ta samu tun farko.
Har yanzu Faransa bata yi rashin nasara ba a dukkanin wasannin sabuwar gasar ta Nations League da take fafatawa, abinda ya bata damar jan ragamar rukunin farko da take ciki da maki 7, Holland ke biye mata da maki 3 yayinda Jamus ke da maki 1.
A jimlace Faransa bata yi rashin nasara ko da sau daya ba, a dukkanin wasanni 14 da ta fafata a baya bayan nan, ciki harda wasanni bakwan da ta buga na gasar cin kofin duniya ta bana da ta lashe.
“Har yanzu babu kasar da takai tamu samun nasara duk da cewa an kammala gasar cin kofin duniya kuma kowacce kasa tayi gyara” in ji Griezman wanda yake bugawa kungiyar Atletico Madrid wasa.

No comments

Powered by Blogger.