Idan Chelsea Tayi Nasara Akan Manchester United, Me Zai Faru Da Mourinho? - Labarai Ingantattu

AdSense

Idan Chelsea Tayi Nasara Akan Manchester United, Me Zai Faru Da Mourinho?

Idan Chelsea Tayi Nasara Akan Manchester United, Me Zai Faru Da Mourinho?
Nasarar da Manchester United ta yi a kan Newcastle ta kawo karshen wasa hudu da ta yi ba tare da nasara baended a run of four games without a win for Jose Mourinho’s team
A ranar Asabar ne Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a Stamford Bridge, a wasan mako na tara na Premier, wanda ke da matukar muhimmanci ga kociyan United din Jose Mourinho ganin irin tsaka-mai-wuyar da yake ciki kan matsayin kungiyar a tebur, inda yanzu take ta takwas da maki 13 a wasa takwas.
Shekara biyu da ta wuce a wannan makon Mourinho wanda ke cikin matsi ya jagoranci kungiyar tasa ta je gidan Chelsea wadda ta casa ta.
A lokacin united tana da maki 14 a wasanninta takwas na farko na gasar, kuma tana matsayi na bakwai a teburin Premier.
Mourinho wanda kungiyar ta dauko da fatan shi ne zai fitar da ita daga halin da take ciki na koma-baya, sai ya kasance bai ba wa marada kunya ba, babu wani sauyi na sosai da ya kawo mata.
A wannan wasa na ranar cikin dakika 30 kacal da take leda Chelsea ta daga ragar bakin nata, kuma zuwa karshen karawar ta casa United da ci 4-0.
Wannan rashin nasara ya zamar wa Mourinho tsohon kociyan Chelsean wanda magoya bayan kungiyar suka rika tsokana, mafi muni a dukkanin wasannin da ya jagoranta tun watan Nuwamba na 2010.
Kuma sakamakon ya kasance mafi muni da United ta gani a gasar Premier a wasan waje tun shekara ta 1999.
To a wannan kakar kuma Red Devils din sun gaza da maki daya a wasanninsu takwas na farko kuma sun yi kasa da mataki daya a teburin gasar ta Premier idan aka kwatanta da wancan lokacin.
Bugu da kari har yanzu ba su hadu da Manchester City da Liverpool ba sabanin a kakar 2016/17 da suka riga suka fafata zuwa yanzu.
To yanzu ga shi za su sake zuwa Stamford Bridge. Idan har Chelsea ta sake maimaita musu abin da ta yi musu a wancan lokacin ta lallasa su, to hakan ba shakka zai kai Mourinho ya baro shi.
A halin yanzu Manchester United tana fuskantar wasa shida wadanda kila su sa ta san matsayinta a bana da kuma makomar kociyanta Mourinho.
Bayan wasanta na ranar Asabar a gidan Chelsea, United din za ta karbi bakuncin Juventus a gasar Zakarun Turai, sannan ta kara karawa a gida da Everton, kafin kuma ta tafi gidan Bournemouth, daga nan ta je ramako Turin gidan Juventus sannan ta kammala da wasan hamayya na Manchester a filin City.

No comments

Powered by Blogger.