Kofin Duniya: Rasha Ta Samu Fam Biliyan 14 A Matsayin Riba - Labarai Ingantattu

AdSense

Kofin Duniya: Rasha Ta Samu Fam Biliyan 14 A Matsayin Riba

Kwamitin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ya lura da shirya gasar cin kofin duniya ta bana, ya ce Rasha mai masaukin baki, ta samu ribar sama da dalar Amurka biliyan 14, sakamakon karbar bakuncin gasar da ta yi.
Shugaban kwamitin na hukumar ta FIFA da ya jagorancin shirya gasar Aledey Sorokin ne ya bayyana alkalumman a wani taro da suka yi a birnin Doha na kasar Katar, domin nazari kan tasirin gasar cin kofin duniyar bana akan tattalin arzikin Rasha.
Kwamitin na FIFA ya kara da cewa gasar cin kofin duniyar ya bada damar samar da sabbin guraben ayyukan yi a Rasha har dubu 315,000, haka zalika tattalin arzikin kasar zai ci gaba da amfana sakamakon daukar nauyin gasar, nan da shekaru 5 masu zuwa.
Tun farkon fara gasar ta cin kofin duniya, wani nazari da akayi ya nuna cewa mutane akalla sama da miliyan daya da rabi ne suka shiga kasar ta Rasha domin kallon wasannin kofin kuma zasu kashe miliyoyin kudi.
Wannan dai shine karo na farko da kasar Rasha ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya tun bayan rugujewar tarayyar sobiyat kuma kasar Faransa ce ta samu nasarra lashe gasar.

No comments

Powered by Blogger.