Monaco ta nada tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry A Matsayin sabon kocinta - Labarai Ingantattu

AdSense

Monaco ta nada tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry A Matsayin sabon kocinta

An nada tsohon dan wasan kwallo na gaba na kungiyar Arsenal, Thierry Henry sabon kocin kungiyar Monaco ta Faransa har zuwa shekarar 2021.
Henry dan kasar Faransa mai shekara 41 da haihuwa ya rike mukamin mataimakin kocin kasar Belgium tun 2016.
Ya fara buga wasan kwallon kafa a kungiyar ta Monaco kuma ya taimaka mata lashe gasar Ligue 1 a 1997.
A yanzu kungiyar na cikin wani mawuyacin hali, domin suna matsayin na uku daga karshe a gasar Ligue 1, matakin da ya sa suka kori kocinsu Leonardo Jardim ranar Alhamis.
Thierry Henry ya bayyana yadda ya ji da aka bayyana shi a matsayin sabon kocin Monaco:
“Da alama kaddara ta riga fata domin gani na dawo kungiyar da na fara buga wasan kwallon kafa a matsayin kocinta”.

Tarihin Gwarzo Thierry Henry

Henry na tare da Belgium a ranar Jumma’a, yayin da suka lallasa Switzerland 2-1 a sabuwar gasar Nations League.
A watan Yuli ne ya taimaka wa Belgium ta kai matakin kasa ta uku a duniya a gasar cin kofin kwallon kafa da aka yi a Rasha.
Ya fara wasan kwallon kafa a Monaco a 1994 a karkashin tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger, kafin ya koma Juventus a 1999.
Bayan shekara daya kacal a Italiya, sai ya koma Arsenal inda ya bayar da gudunmawarsa ta lashe gasar firimiya biyu da kofin FA biyu a shekaru takwas da yayi a kungiyar da ke arewacin Landan.
Daga Arsenal sai ya koma Barcelona inda ya lashe La Liga da Copa del Rey da kuma Champions League a kakar wasa daya, wato 2008-2009.
A 2010 sai ya koma kungiyar Red Bulls ta league din MLS a Amurka, inda ya shafe kakar wasa biyar, koda yake ya koma Arsenal na wata biyu a 2012.
Henry ya lashe kofin duniya a 1998 da kungiyarsa ta Faransa, ya kuma lashe gasar kasashen Turai a shekarar 2000 inda a jimilla ya zura kwallo 51 a wasanni 123 da ya buga wa kasarsa.
A watan Disambar 2014 ne yayi ritaya daga buga wasan kwallo, kuma da farko ya fara yin bayanin wasannin kwallo ne a tashoshin talabijin kafin ya koma aikin horaswa da kungiyar Belgium. a 2016.

No comments

Powered by Blogger.