Mun Mika Sunayen ‘Yan Takara Daga Zamfara — APC - Labarai Ingantattu

AdSense

Mun Mika Sunayen ‘Yan Takara Daga Zamfara — APC

A Najeriya yayin da wa’adin mika sunayen ‘yan takarar majalisar dokokin tarayya ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ya kare a daren ranar Alhamis, hukumar zaben ta ce tana nan kan bakanta game da kin amincewa da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC daga jihar Zamfara, duk kuwa da wani hukunci da kotu ta yanke a kan al’amarin.
Hukumar ta ce a ta ta fahimtar umarnin kotun yana nuni ne da cewa kowa ya tsaya a kan matsayin da ya dauka.
Wata babbar kotu ce a jihar Zamfara ta bayar da wani umarni na wucin gadi, wanda ya hana hukumar zabe ta kasar INEC da jam’iyyar APC haramta wa ‘yan takarar jam’iyyar na kujerun gwamna da majalisar dokoki ta tarayya da na jihar, shiga babban zaben da za a yi a badi.
Wasu shugabannin reshen jam’iyyar APC na jihar Zamfara ne suka shigar da karar, bayan hukumar zaben ta hana jam’iyyar gabatar da sunayen ‘yan takarar na ta na jihar, saboda rashin gudanar da zabukan fitar da gwani.
To sai dai kuma a nata bangaren, jam’iyyar APC, ta ce tuni ta mika wa hukumar zaben sunayen ‘yan takararta na ko ina har ma da na jihar Zamfarar.
Jami’in kula da walwalar jama’a na jam’iyyar na kasa Ibrahim Masari, ya shaida wa BBC cewa tun kafin karfe biyar na yammacin ranar cikar wa’adin jam’iyyarsu ta kai sunayen ‘yan takararta hukumar zaben kuma har da na jihar Zamfara.
Ibrahim Masar ya ce, ‘ Hakkinmu ne da iko na jam’iyya ta kai suna kuma sun kai sunayen, batun ko suwa muka kai sunayensu daga Zamfara, sai a jira sai hukumar zaben ta fitar da sunayen a gani’.
Karin bayani
Rikicin siyasa a Zamfara dai ya kara zafi ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.
Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha’awar takarar gwamnan a jam’iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.
Sau biyu anashirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke shi saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam’iyyar a jihar.

No comments

Powered by Blogger.