NLC Da TUC Sunyi Barazanar Fara Sabon Yajin Aiki Sabida Karin Albashi - Labarai Ingantattu

AdSense

NLC Da TUC Sunyi Barazanar Fara Sabon Yajin Aiki Sabida Karin Albashi

Karin albashi: NLC da TUC sunyi barazanar fara sabon yajin aiki
Kungiyoyin Kwadago na kasa (NLC) da Kungiyar Masu Sana’o’i (TUC) sunyi barazanar sake fara wani sabon yajin aiki saboda batun karin albashi na ma’aikata mafi karanci a Najeriya.
Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana cewar akwai yiwuwar ma’aikatan za su koma yajin aiki cikin kankanin lokaci bayan an gudanar da taro domin tabbatar da cewa ma’aikatan ba za su cutu ba.
Kazalika, Wabba ya cacaki Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige inda ya ce ministan ya yi gaban kansa ne wajen fadin cewar gwamnati ba za ta iya biyan N30,000 ba kuma kungiyarba za ta amince da wani canji kan hakan ba.
A hirar da ya yi da manema labarai a birnin Lokoja wajen kaddamar da gidaje 1,200 na ma’aikatan Bankin bayar da bashin gina gidaje (FMBN), Wabba ya ce abinda Ngige ya fadi ya sha ban-ban da yarjejeniyar da kwamitin albashin ta tsayar.
A ranar Laraba, Ministan ya ce har yanzu ba’a tsayar da adadin albashin mafi karanci da za’a iya biya ba saboda har yanzu ana tattaunawa a maimakon abinda kungiyar kwadago ta fadi na cewar gwamnati ta amince za ta biya N30,000.
Sai dai shi a bangarensa, Wabba ya ce an cimma matsaya kan albashin da za’a biya kuma duk wanda ya ce ba’a cimma matsaya ba, ba gaskiya ya ke fada ba.
A bangarensa, Shugaban TUC, Boboi Bala Kai Gama, ya ce ya yi matukar mamakin yadda gwamnatin tarayya za ta canja alkawarin da tayi kan albashi mafi karanci.

No comments

Powered by Blogger.