Sanarwar Gagarumin Taro Da Wa`azi A Birnin Abuja - Labarai Ingantattu

AdSense

Sanarwar Gagarumin Taro Da Wa`azi A Birnin Abuja

Sanarwar Gagarumin Taro Da Wa’azi A Birnin Abuja

Hukumar gudanarwa na gidan Talabijin da Rediyo na MANARA ta shirya gagarumin taro a karshen makon nan a birnin tarayya Abuja.

Taron na kwana daya zai ta’allaka ne kan Bita (Symposium) akan illolin shan miyagun kwayoyi da sauran shaye shaye ga al’umma.

Za’a gabatar da taron ne ranar asabar 10-Safar-1440, 20-Oktoba-2018 da misalin karfe goma na safe (10:00am) a babban dakin taro na kasa da kasa (International Conference Center) dake Area 10 a cikin birnin tarayya Abuja.

Taken taron shine “Shan Miyagun Kwayoyi, babban kalubale ga tsaro da cigaban kasa da yadda za’a magance matsalar”.

Kazalika Kungiyar zata gabatar da gagarumin wa’azi anan cikin Abuja, ranar juma’a 09-Safar-1440, 19-Oktoba-2018, Wanda kusan dukkan Malaman kungiyar zasu halarta, insha Allahu.

Kazalika, a ranar asabar din bayan antashi taron Bita, Kwamitin tattara fatun layya karkashin jagorancin Shugaban kwamitin, Sheikh Habibu Yahaya Kaura Za su gabatar da Rahoton adadin fatun layya da suka tattara a babbar sallar data gabata, da jimillar kudin fatun, zuwa ga majalisar koli ta JIBWIS, Wanda shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau da sauran yan majalisar zasu karba.

Wadanda ake bukata a wurin taron sun hada da dukkan shugabannin Kungiya, shugabannin Malamai da daraktocin Agaji a matakin Jihohi, da kuma jami’an “Jibwis Social Media” a matakin kasa (National Exco).

Allah ya bada ikon zuwa, Amin.

Sanarwan ta fito ne daga sakataren kungiyar JIBWIS Sheikh Kabir Gombe, ta ofishin Darakta Social Media na kasa, Ibrahim Baba Suleiman.

The post Sanarwar Gagarumin Taro Da Wa`azi A Birnin Abuja appeared first on ArewaBlog.Com™.

No comments

Powered by Blogger.