Sheikh Saeed Ibn Wahl Al-Qahtani: Malamin da ya rubuta littafin 'Hisnul Muslim' ya rasu - Labarai Ingantattu

AdSense

Sheikh Saeed Ibn Wahl Al-Qahtani: Malamin da ya rubuta littafin 'Hisnul Muslim' ya rasu

Masani kuma marubucin littafai addini ya rasu  safiyar ranar Litinin 1 ga watan oktoba a babban birnin Riyadh na kasar Saudi Arabia.

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Saeed ibn Wahl Al-Qahtani ya rasu.

Masani kuma marubucin littafai addini ya rasu  safiyar ranar Litinin 1 ga watan oktoba a babban birnin Riyadh na kasar Saudi Arabia.

Anyi jana'izar shi a masallacin Rajhi bayan sallar la'asar na ranar.

Shehin malamin ya rubuta littafai da dama na musulunci. daya daga cikin litaffai da ya rubuta shine shahararren littafin addu'o'i mai suna 'Hisnul Muslim' wanda aka yi ma fassarar 'Garkuwan musulmi' da harshen hausa.

An wallafa litaffin da harsuna daban-daban dake fadin duniya.

Shehin Malamin ya rasu bayan ya sha fama da ciwon daji.

No comments

Powered by Blogger.