`Yan Shi`a Sun Nemi Ganin Buhari Akan Sheik Zakzaky - Labarai Ingantattu

AdSense

`Yan Shi`a Sun Nemi Ganin Buhari Akan Sheik Zakzaky

‘Yan Shi’a Sun Nemi Ganin Buhari Akan Sheik Zakzaky
Daga Bilya Hamza Dass
Kimanin shekara guda kenan ‘yan Shi’a sun maida Abuja tamkar gida a wajansu a inda suka maida kowacce rana suna fitowa a manya manyan titunan garin suna masu nuna bukatar su kan cewa a sake Malamin su Sheik Zakzaky wanda ke tsare kimanin shekaru uku, tun bayan a rangamarsu da sojoji a watan Disambar 2015 a garin Zaria.
Daga bisani salon nasu ya fara canzawa inda suka fara rubuce-rubuce a manyan allunan talla da kuma jikin gine-ginen gwamnatin na batanci ga Shugaba Buhari da gwamnatinsa.
Kwanakin baya sun je ma’aikatar Sharia suka rufe suna masu fadin ba a yi musu adalci ba. Ko a makonni biyu da suka gabata, dandazon ‘yan Shi’a sun nufi fadar Shugaban kasa wato Villa, inda suka dinga ikirarin sai sun je da karfi, suna masu fadin a sake musu Malaminsu.
A bangaren jami’an tsaro sun hana su shiga sun nemi da su kawo a rubuce cewa suna so su ga Buhari akan Malaminsu. Inda a yau suka rubuta takardar suka mika ga jami’an tsaro da alkawarin za su mika korafin ga shugaba Buhari.

No comments

Powered by Blogger.