Yau Ne Cigaba Da Sauraren Karar Gwamnatin Katsina Kan Shema a Kotu - Labarai Ingantattu

AdSense

Yau Ne Cigaba Da Sauraren Karar Gwamnatin Katsina Kan Shema a Kotu

KATSINA STATE MASARI MEDIA ENLIGHTENMENT FORUM
Daga Falalu Lawan
Kai tsaye daga Babbar kotun jahar katsina
A yau ne ake cigaba da sauraron karar da gwamnatin jahar katsina ta shigar akan zargin tsohon gwamna shema akan kasa da fadi da wasu makuddan kudi da suka Kai kimanin naira billion goma sha daya.
Yanzu an dawo har an ci gaba da shara’ ar lauyan gwamnati yace a Basu dama su fara gabatar da shaidun da suka zo dasu
Lauyan shema ke magana Yana fadin akwai Karar da shema ya shigar a kotun daukaka Kara da ke kaduna .
Yace sun shigar,kuma an Sanar da duk wadanda abin ya shafa
Yace a karar mun nemi a dakatar da wannan shara ar da ake a wannan kotun har sai an Gama sauraren korafin mu dake babbar kotun kaduna Wanda za a saurara a ranar 21/10/2018.
Don Haka muna bukatar da wannan kotun ta dakata har sai kotun kaduna ta gama sauraren koken da aka Kai mata.
Lauyan yace na dogara da wasu Shari un da akayi a baya,kuma ya karanta duk madogarar ta sa.
Lauyan shema; bisa hujjojin nan muna son a tsaida shara ar nan sai an gama sauraren karar da muka shigar a kotun kaduna.
Lauyan shema ya zauna wani Cikin lauyoyin na shema ya Mike ya kara jaddada waccar matsayin na lauyan Farko.
Bayan duk sun gama kawo hujjojin su, Yanzu lauya EFCC ya mike domin rosa duk hujjojin da lauyoyin shema da dankaba suka kawo.

No comments

Powered by Blogger.