Yunkurin Shugaba Buhari Na Magance Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya - Labarai Ingantattu

AdSense

Yunkurin Shugaba Buhari Na Magance Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya

Yunkurin Shugaba Buhari Na Magance Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya
Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nisa a shirin ta na bunkasa gidajen yarin dake fadin kasar nan.
Inda Gwamnatin tarayya za ta gina gidan yari mai daukar mutane dubu uku (3,000) a shiyoyi shida da muke da su a cikin kasar nan.
Cibiyar yada labarai na shugaba Buhari (BNMCVolunteers) ta kai ziyarar gani da ido a daya daga cikin gidan yarin a jihar Kano.
Samar da sabbin gidajen yarin a shiyoyin na Nijeriya, zai taimaka wajen rage matsalar cinkushewar ‘yan fursuna a fursunonin kasar nan.
Shugaba Buhari ya gano cewa akwai bukatar bunkasa gidajen yarin Nijeriya, wanda hakan ya sa a watan Disamba na shekarar 2017, gwamnatin tarayya ta soma gina wannan gidan yari mai cin mutane 3,000 a Janguza dake jihar Kano, inda an kammala kusan kashi tamanin daga cikin dari.
An gina gidan yarin na Kano mai daukar mutane 690 a shekarar 1910, amma a yanzu ‘yan fursunan dake ciki sun kai kusan 2000, wada hakan ya sanya shugaba Buhari ya nuna damuwar sa game da hakan, inda a watan Yuli na wannan shekara ya umarci ministan shari’a Abubakar Malami domin yin duba kan matsalar cunkushewar gidajen yarin.
Biyo bayan umarnin na shugaban kasa, ministan shari’a ya kafa kwamitin mutane 18 karkashin jagorancin Alaklin Alkalai na kasa, Ishaq Bello, inda kwamitin ya ‘yanta ‘yan fursuna 1,310 wadanda suke da kananan laifuka da aka ci su tara.
Yanayin da gidajen yarin na Nijeriya ke ciki ya zama babbar barazana ga ‘yancin wadanda ke tsare a gidajen yari, amma bisa yunkuri shugaba Buhari na magance matsalar, za a kawo karshen matsalolin nan bada jimawa ba.
Bashir Ahmad
Shine Hadimin Shugaban
Kasa kan kafafun sadarwa
Kuma Ko’adineta Na Kasa
Na Cibiyar Yada Labaran
Shugaba Buhari (BNMC)

No comments

Powered by Blogger.