Zaben fidda gwani: Adams Oshiomole ya amince da sakamakon zaben Legas - Labarai Ingantattu

AdSense

Zaben fidda gwani: Adams Oshiomole ya amince da sakamakon zaben Legas

APC National Chairman, Adams Oshiomole

Oshiomole ya kawar da labarin soke zabe da kwamitin mai sa ido tayi inda yace an gudanar da zaben jihar kamar yadda ya kamata.

Shugaban jam'iya mai mulki ta APC, Adams Oshiomole ya amince da sakamakon zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Legas ranar Talata.

Oshiomole ya kawar da labarin soke zabe da kwamitin mai sa ido tayi inda yace an gudanar da zaben jihar kamar yadda ya kamata.

A labarin da gidan telibijin ta TVC ta fitar, shugaban jam'iyar ya sanar da matsayar shi game da zaben bayan ganawar da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban.

Kwamitin ta soke zaben bisa ga zargin fuskantar zagon kasa da magudi.

APC ta jihar Legas ta kaddamar da Sanwo-Olu a matsayin wanda yayi nasara

Shugaban jam'iyar APC na jihar Legas, Tunde Balogun, ya sanar da sakamakon zaben tare da kawar da labarin soke zaben da kwamitin uwar jam'iyar tayi.

A sanarwar da ya fitar, Sanwo- Olu ya dankari gwamna mai saman kujera da kuri'u mafi rinjaye.

Babajide Sanwo-Olu ya samu kuri'u 970, 851 yayin da gwamna Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72, 901 cikin kuri'u sama da miliyan daya da aka kada.

Bisa ga wannan sakamakon shugaban ya kaddamar da Sanwo-Olu a matsayin wanda zai daga tutar APC a zaben 2019.

No comments

Powered by Blogger.