Zaben fidda gwani: Ganduje zai fafata da surukin kwankwaso a zaben gwamnan Kano - Labarai Ingantattu

AdSense

Zaben fidda gwani: Ganduje zai fafata da surukin kwankwaso a zaben gwamnan Kano

Abba K. Yusuf ya doke tsohon mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafeez Abubakar da Salihu Sagir Takai wajen zama gwanin PDP a zaben 2019 dake gabatowa.

Jma'iya mai mulki ta APC da babban jam'iyar adawa, PDP sun gudanar da zaben gwani na takarar gwamnan Kano a karshen makon da ya gabata.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya lashe zaben APC na neman zarcewa a saman kujerar da yake kai. Ya lashe zaben jam'iyar da kuri'u mafi rinjaye.

A bangaren PDP kuwa, dan takarar Kwankwaso yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na PDP.

Abba K. Yusuf ya doke tsohon mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafeez Abubakar da Salihu Sagir Takai wajen zama gwanin PDP a zaben 2019 dake gabatowa.

Ya samu kuri'u 4000 yayin da Takai ya samu 307 sai kuma farfesa Hafiz wanda ya samu kuri'u 70.

Kwankwaso ya tsayar da surukinsa a matsayin dan takarar PDP

Kwankwaso wanda ke neman kujerar shugaban kasa ya tsayar da mijin diyar shi, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda zai daga tutar PDP a zaben 2019 sabanin yadda jama'a suka yi tunani duba da irin goyon bayan da tsohon matimakin gwamnan jihar na yanzu da kuma Takai wanda ya fito takarar kujerar a zaben 2015.

Da yake zantawa da manema Labarai yayin da ya kai ziyara Kano ranar Litinin 24 ga wata, Kwankwaso yayi ikirari cewa surukin tasa ba mijin-hajiya bane domin yana da mata biyu kuma yadda matar sa zata juya shi.

A labarin da Daily Nigerian ta fitar, tsohon gwamnan yace masu korafi game da takarar wanda ya tsayar su mayar da hankalin su wajen gani ko ya cancanta.

Kwankwaso ya ce bayan nazari da tuntuba da shawara da suka yi da mutane da dama tsawon shekara uku da doriya domin duba wanda ya kamata su tsayar a takara ba tare da an sake maimaita abin da ya faru ba na sabani da matsalolin da suka samu kansu a ciki, kuma yawanci suka nuna cewa Abba K. Yusuf ne ya fi dacewa.

No comments

Powered by Blogger.