Zaben fidda gwani: Tsohon mataimakin kakakin majalisa ya lashe zaben PDP - Labarai Ingantattu

AdSense

Zaben fidda gwani: Tsohon mataimakin kakakin majalisa ya lashe zaben PDP

A zaben da aka gudanar ranar litinin, Nafada ya doke sauran yan takara 12 da suka yi takara dashi.

Tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya kuma dan majalisar dattawa,  Sanata Bayero usman Nafada, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyar PDP na takarar gwamnan jihar Gombe.

A zaben da aka gudanar ranar litinin, Nafada ya doke sauran yan takara 12 da suka yi takara dashi.

Ya samu kuri'u 1104 cikin kuri'u 1320 da aka kada wajen lashe sakamakon zaben.

Babban jami'in PDP da ya sa'ido ga zaben jihar, Joe Akaka, ya sanar da dan majalisar a matsayin wanda yayi nasara a zaben ranar talata 2 ga watan Oktoba.

Yan takara da suka fafata wajen zama gwanin PDP a jihar sun hada da,Jamilu Isiyaku Gwamna, Abubakar Walama, Hassan Muhammadu, Bala Bello Tinka, Gen Sylvester Audu, Abbakar Bappah Musa, Senator Haruna Garba, Ahmed Mohammed Goje, Katukan Gombe, Umar Bello, Alhassan Mohd Fawu da Abdulkadir Hamma Saleh.

Daya da cikin yan takarar, Mallam Bala Tinka, wanda yayi magana a madadin sauran yan takara yace zasu cigaba da mara ma wanda yayi nasarar baya domin lashe zaben jihar a 2019.

Yayin da yake jawabi, Nafada yayi alkawarin aiki da sauran yan takarar domin cinma manufar yin nasara a zaben dake gabatowa.

No comments

Powered by Blogger.